
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta bayyana cewa daga 1 zuwa 15 ga watan Satumba, akwai yiwuwar ambaliya ta shafi jihohi 29 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Rahoton ya ƙara da cewa lamarin zai iya shafar ƙananan hukumomi 107, garuruwa 631 da tituna 50 a sassa daban-daban na ƙasar.
Hukumar ta bayyana cewa jihohin da suka fi shiga cikin hatsari sun haɗa da: Borno, Zamfara, Jigawa, Kebbi, Yobe, Filato, Gombe, Taraba da Sakkwato, yayin da a Jihar Kaduna barazanar ambaliyar ba ta da yawa.
NiHSA ta shawarci al’ummomi da hukumomi a yankunan da aka ambata su ɗauki matakan kariya tun da wuri, domin gujewa illolin ambaliyar da ka iya shafar rayuka da dukiyoyi.
