
15 Satumba, 2025
Daga Mutawakkilu Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, tare da haɗin gwiwar kungiyoyin fararen hula (CSOs), ta gudanar da babban taro a jihar domin ƙarfafa haɗin kai da inganta shugabanci nagari.
Da yake bude taron, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakinsa, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, ya wakilta, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da gina kyakkyawar dangantaka da kungiyoyin fararen hula a matsayin abokan tafiya wajen tabbatar da gaskiya, rikon amana, da cigaban jama’a.
Ya bukaci kungiyoyin CSOs da su ci gaba da zama jakadu na gaskiya, su guji cin hanci da rashawa tare da raba kansu da duk wani abin da zai gurbata aikinsu. Gwamnan ya kuma ja hankalinsu da su kara himma wajen wayar da kan al’umma kan illolin dabi’u marasa kyau, musamman matsalar ‘yan daba, yaɗa labaran karya, da sauran abubuwan da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro.
“Muna kira gare ku da ku kasance masu ba da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna a fadin jihar Kano,” in ji shi.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kungiyoyin fararen hula, tare da inganta ayyukan cigaban al’umma.
Ya kara da cewa gwamnatin Gwamna Yusuf tana tafiyar da mulki na gaskiya da amana, tana kuma maraba da shawarwari da sukar da aka yi cikin gaskiya da nufin kyautata ayyukan gwamnati.
Taron, mai taken “Karfafa Kungiyoyin CSOs a Kano Don Dorewar Dimokuradiyya da Cigaban Kasa”, ya tattaro mahalarta daga cikin jihar da wajen ta, ciki har da wakilan kungiyoyin fararen hula, masu aikin jarida, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
