By Khadijah Shehu Abdulkareem

Gwamnan ya kuma ce ya san dukkan inda ’yan bindigar jihar suke buya.
Da yake jawabi a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, gwamnan ya ce babban kalubalen shi a yaki da ’yan bindiga a jihar shi ne rashin cikakken iko da jami’an tsaro.
Ya ce shugabannin rundunonin tsaron da ke jihar suna karbar umarni ne kawai daga hedkwatocinsu da ke Abuja, ba daga wajen shi ba.
