
By Mutawakkilu Ibrahim
Shugaban kwamitin wayar da kan al’uma akan muhimmancin yin katin zaben kuma kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Comred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a yayin taro na musamman daya gudana da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu na jihar.
Ayayin taron kwamishina Waiya ya bayyana rashin Jin dadinsa bisa yadda jihohin kudancin Kasar nan suka yi wa jihar Kano nisa wajen yawan mutanen da suka yi rijista daga lokacin da aka sake bada damar sabunta rijistar, yace ya zama wajibi a kawar da batun siyasa domin sanya cigaban jihar a gaba.
Yace Kano wacce ita ce jiha mafi yawan al’uma a kasar nan, amma ana neman barinta a baya idan aka kwatanta da jihohin kudu wadanda zuwa yanzu sun yiwa jihar Kano tazara ta fuskar yawan wadanda suka yi rijista.
Ya bayyana muhimmanci mallakar katin zabe wajen tabbatar da ingantacciyar dimokuradiyya, don haka ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da shugabannin dana kungiyoyin sa-kai dasu tallafawa yunkurin gwamnati don ganin jihar Kano ta rike kambunta na jihar da tafi kowace yawan al’uma a kasar nan, ya zamto tafi yawan wadanda suka mallaki katin zabe.
Kwamishina waiya yace har yanzu wadanda sukayi rijistar mallakar katin zabe a jihar Kano ba su wuce dubu 10 ba, yayinda wasu jihohin Kudu suka yiwa mutane sama da dubu 300.
Don haka, ya yi kira ga daukacin al’umar jihar Kano da su fito su yi rijistar katin zabe domin kada su rasa damar su ta zabar shugabanni na gari a zabuka masu zuwa.
Kwamishina Waiya ya kara da cewa gwamnati ta zabi ta kulla alaka da kungiyoyi masu zaman kansune la’akari da guduwamar da suke bayarwa wajen hada Kan al’uma da cigabansu.
A nasa bangaren shugaban gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na jihar Kano Comred Hassan Ibrahim Gama yace a shirye suke su yi amfani da kungiyoyin su wajen wayar da kan al’umar jihar Kano su fito su mallaki katin zabensu a lungu da saƙo na jihar Kano.
Ya ce zasu yi amfani da kungiyoyinsu wajen tabbatar da an yiwa mutane miliyan goma rijistar a jihar Kano.
Taron ya samu halartar kungiyoyin fararen hula dake fadin jihar Kano.
