
By Mutawakkilu Ibrahim
Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida Comred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya jagoranci kaddamar da kwamitin a ofishinsa dake audu bako sakateriya.
Waiya ya ce an kafa kwamitin ne domin samar da wani zaure da zai fitar da ka’idoji da dokokin yada labarai a jihar Kano da nufin tsaftace harkar daga munanan kalamai da cin zarafi da kuma kaucewa kalaman da suka ci karo da tarbiyya da al’ada na mutanan jihar.
Yace an dorawa kwamitin alhakin fitar da shawarwari Kan yadda zauren zai kasance da kuma bayanin wadanda ya kamata su zama wakilai a cikin kwamitin.
A nasa bangaren shugaban kwamitin wanda ya kasance tsoho kuma gaggen Dan jarida Alhaji Ahmad Aminu ya ce kwamitin zai yi aiki tukuru domin fito da yadda zauren da za a kafa zai kasance domin tsaftace al’amuran yada labarai a jihar Kano.
Wakilan kwamitin sun hada da Alhaji Ahmad Aminu a matsayin shugaba da Alhaji Muhd. Danyaro da Alhaji Abdulkadir Ahmad Kwakwatawa da Prof. Umar farouk Jibril.
Sauran sun hada da Dr. Halima Musa Kamilu da Dr. Sule Yau Sule da Dr. Saminu Umar Rijiyar Zaki a matsayin Sakataren kwamitin, da kuma Mustapha Gambo da Hauwa Sulaiman Zahraddeen a matsayin wakilai daga Kungiyar Yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano.
